5 Janairu 2022 - 14:23
​Vienna: Wakilan Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Batutuwan Da Ba A Warware Su Ba

Wakilin kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna na kasar Austiria ya bayyana cewa, ya tattauna batutuwan da ba a cimma matsaya a kansu ba da shugaban tawagar Iran a Vienna a ranar jiya Talata kan farfado da yarjejeniyar nukiliya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wakilin kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa da ke birnin Vienna na kasar Austria Mikhail Ulyanov ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, ya gana da yammacin jiya Talata da Ali Bagheri Kani, babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar Vienna.

Ya Ce: "Na gana da Dr. Ali Bagheri Kani, shugaban tawagar Iran kuma mataimakin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran," kamar yadda ya rubuta a cikin sakon nasa a shafin Twitter.

Ulyanov ya kara da cewa, "Mun tattauna kan manyan batutuwan da ba a warware su ba, wadanda ya kamata a warware su yayin tattaunawar Vienna don farfado da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a 2015."

A ranar jiya Talata 4 ga watan janairu, an ci gaba da zama zagaye na takwas na shawarwarin dage takunkumin da aka kakabawa kasar Iran a birnin Vienna.

Ali Bagheri da tawagar da ke masa rakiya sun isa Vienna don ci gaba da tattaunawa tare da sauran bangarorin yarjejeniyar wato (Jamus, Faransa, Rasha, Sin da Birtaniya) da kuma wakilan kwamitin hadin gwiwa na kwamitin sulhu na MDD gami dad a wakilan kungiyar Tarayyar Turai.

342/